Faransa-Rasha

Faransa ta zargi Rasha da yunkurin yi mata leken asiri

Ministar Tsaron Faransa Florence Parly.
Ministar Tsaron Faransa Florence Parly. CHARLY TRIBALLEAU / AFP

Ma’aikatar tsaron Faransa ta yi ikirarin cewa Rasha ta yi yunkurin yi mata leken asiri a bara ta hanyar na’urar Satellite inda ta yi kokarin nadar tattaunawar ma’aikatar sojinta.

Talla

Ministar tsaron Faransa Florence Parly ta ce Rashan ta yi amfani da Na’urar Satellite ta hadin gwiwa tsakaninta da Italiya wajen nadar wasu tarin tattaunawa a ma’aikatar tsaron kasar ta hanyar amfani da na’urarta ta Luch-Olymp craft mafi karfi wajen iya satar zance.

Parly wadda ke sanar da hakan a ziyarar da ta kai cibiyar nazarin ilimin sararin samaniya da ke birnin Toulouse a kudancin Faransa, ta ce matakin nadar zantawar da Rasha ta yi ba wai kawai abu ne da za a kira da bai dace ba a a yunkuri ne na leken asiri.

Acewar ministan tsaron ta Faransa sun dauka kwararan matakan ganin Rashan bata yi musu kutse wajen samun bayanansu kan tsaro ba, haka zalika ta sha alwashin mayar da kakkausan martini kan Rashan wadda ta ce leken asirin da ta ken a da matukar hadari.

Ko a watan da ya gabata ma, Amurka ta zargi Rashan da samar da wasu nau’ikan makamai ta na’urar Satellite ciki har da wasi makami da ba safai aka saba ganin irinsa ba da Rashan ta kirkira a watan Oktoban bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.