Faransa

Maharin wuka ya raunata mutane a Paris

Jami'an 'yan sanda na bincike a wurin da harin ya auku
Jami'an 'yan sanda na bincike a wurin da harin ya auku 路透社

Akalla Mutane 7 suka samu rauni, cikin su har da baki ‘yan yawon bude ido guda biyu daga Birtaniya lokacin da wani mutum ya kai musu harin wuka a birnin Paris.

Talla

Majiyar ‘yan sanda ta bayyana wanda ya kai harin a matsayin wani dan asalin kasar Afghanistan kuma tuni aka kama shi.

Majiyar ta ce, ya zuwa yanzu babu abin da ke danganta harin da ayyukan ta’addanci.

Bayanai sun ce, 4 daga cikin wadanda aka kai wa harin na cikin mawuyacin hali.

Rohotanni sun ce, kimanin mutane 20 suka yi kokarin hana maharin ta hanyar jifan sa da kananan kwallayen wasan petanque da suka same shi a ka, amma duk da haka bai hanu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.