Faransa

'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga a Faransa

Masu zanga-zangar na adawa da matakin gina wata babbar hanyar motoci a Faransa
Masu zanga-zangar na adawa da matakin gina wata babbar hanyar motoci a Faransa Reuters/路透社

Rundunar ‘yan sandan Faransa ta yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa kimanin mutane 200 da suka datse wata babbar hanyar da ake kan ginawa a kusa da gabashin birnin Strasbourg a yayin wata zanga-zanga.

Talla

A cikin watan Agustan da ya gabata ne, mahukuntan yankin suka amince da fara gina hanyar motocin mai tsawon kilomita 24, amma masu adawa da aikin ginin sun ce, zai lalata gonaki tare da yi illa ga muhalli har ma da wasu nau'ukan halittu.

Masu zanga-zangar da suka kira kansu da suna “Zadistes” sun kafa shingen katako da tayoyi tun daga farkon hanyar har zuwa kauyen Kolbsheim mai tazarar daruruwan mitoci.

A sanyin safiyar ranar Litinin ne ‘yan sanda dauke da garkuwa suka tarwatsa taron masu zanga-zangar da ke rajin kare muhalli.

‘Yan sandan sun kuma yi amfani da zarto wajen yanka shigayen da masu zanga-zangar suka kafa.

A watan jiya ne, da dama daga cikin masu gwagwarmayar kare muhalli a Faransa suka yi kira ga tsohon Ministan Muhalli , Nicolas Hulot da ya dakatar da ginin hanyar saboda barazana ga muhalli.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.