Wasanni-kwallon kafa

Zidane na gab da dawowa fagen horar da kwallo

Tsohon kociyan Real Madrid Zinadine Zidane.
Tsohon kociyan Real Madrid Zinadine Zidane. REUTERS/Gonzalo Fuentes

Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid mai doka gasar La Lliga da ke Spain, Zinadine Zidane ya tabbatar da cewa yana gab da dawowa fagen horar da ‘yan wasa ko da dai bai bayyana ko kai tsaye Real Madrid zai koma ba ko kuma zai kulla kwantiragi ne da wata kungiya ta daban.

Talla

Zidane wanda ya sanar da ajje mukaminsa na horar da Real a wani yanayi na bazata kwanaki biyar bayan ya kai kungiyar ga nasarar lashe kofin zakarun Turai karo na 3 a jere, ya ce nan gaba kadan zai dawo fagen tamaula tare da sanar da Club din da zai koma.

Akwai dai rade-raden da ke cewa Zinadine Zidane na tattaunawa da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United don maye gurbin Jose Mourinho da shi a Club din wanda ke fuskantar koma baya.

A wata ganawa da manema labarai Zidane ya ce yana kaunar kwallo kuma yana fatan kare rayuwarsa yana bayar da gudunmawa ga bangaren na Tamaula. 

Zidane dai ya fara horar da karamar tawagar Real Madrid a 2014 kafin daga bisani a mika masa ragamar babbar tawagar a 2016 bayan korar Rafael Benitez inda a shekarar ya kai ta ga nasarar lashe kofin Laliga amma kuma a kakar da ta gabata ta gaza kai labara inda ta tsaya a matsayin ta 3 da maki 17 kasa da abokiyar dabinta Barcelona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.