Faransa-Belgium

Motocin sun kauracewa titunan Paris da Buxelles domin takaita dumamar yanayi

Pedestre nas ruas de Bruxelas, que, assim como Paris, participou do "Dia sem carro" em 16 de setembro de 2018.
Pedestre nas ruas de Bruxelas, que, assim como Paris, participou do "Dia sem carro" em 16 de setembro de 2018. REUTERS/Eric Vidal

A yau lahadi 16 ga watan Satumba, manyan titunan birnin paris sun kasance a rufe ga motoci da kuma babura, a yayinda yan kafa suka mamayesu albarkacin kwana na hudu na ranar hana amfani da ababen hawa masu fitar da hayaki.Dokar hana amfani da motar ta fara ne daga karfe 9 na safe zuwa 4 na yammacin jiya lahadi ta shafi dukkanin motocin hawa,baya ga motocin asibiti da na jam’ian tsaro agajin gaggawa, da na jigilar masu yawon a ido da taxi.

Talla

Manufar wannan rana ta hana hawan da motoci shine, domin rage fitar da hayaki mai gurbata yanayin mahallin jama’a, kamar yadda shafin internet na ma’aikatar magajin garin birnin na Paris ya sanar.

Ofishin magajin garin birnin Paris da ya share tsawon shekaru yana kokowa da gurbatar yanayi, a ranar juma’ar da ta gabata ne, ya bayyana yankuna 4 na farko a birnin na Paris, da suka hada unguwanin (îles de la Cité, Saint-Louis, Châtelet, Louvre, Opéra, Marais, da dai sauransu.) cewa daga ranar 7 ga watan octoban mai zuwa, za su dinga dakatar da zirga zirgar motoci akan manyan titinan da suka hadasu a ko wace ranar lahadi sau daya a wata

Sakamakon gurbatar yanayin dake da illa ga koshin lafiyar al’amma, magajiyan garin biranen Paris Anne Hidalgo da Philippe Close, Bruxelles, a kasar Beljiyom da can ma ake gudanar da irin wannan salo na taikata abababen hawa, sun bada shawarar ware wata rana guda a shekara da zata zama ranar kin amfani da nahiyar Turai

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.