Birtaniya-Turai

Ba za mu amince da bukatar May ba- EU

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai  Donald Tusk
Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Donald Tusk JOHN THYS / AFP

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai, Donald Tusk ya ce, bukatar da Firaministar Birtaniya Theresa May ta gabatar ta kulla sabuwar dangantakar kasuwanci da kungiuar EU ba za ta samu karbuwa ba.

Talla

Tusk wanda ke magana jim kadan da kammala taronsu a birnin Salzburg ya ce, shirin na May na barazana ga tsarin kasuwancin bai-daya na kungiyar kasashen Turai.

Taron ya samu halartar shugabannin kasashen Turai 27 don tattaunawa kan batun ficewar Birtaniya.

A cewar May, shirin nata ne kadai mafita daya tilo wajen kauce wa tsattsauran matakan kan iyakar arewacin Ireland.

Firaministar ta kara da cewa, Birtaniya na da wasu shirye-shirye a kasa ko da an gaza cimma wata yarjejeniya tsakaninta da EU.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.