Venezuela

Maduro zai nemi tallafin dala miliyan 500 daga MDD

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro, ya ce zai nemi majalisar dinkin duniya ta bashi tallafin dala miliyan 500, domin taimakawa gwamnatinsa wajen maido da dubban ‘yan kasar da suka tsrrewa munin halin da durkushewar tattalin arzikin kasar.

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro.
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro. ©Miraflores Palace/Handout via REUTERS
Talla

Shekaru hudu kenan bayan da tattalin arzikin kasar Venezuela ya fada cikin mawuyacin hali , inda a halin masana suka yi hasashen cewa, hauhawar farashin kayayyakin masarufi a kasar ka iya kaiwa kashi miliyan daya bisa dari.

Wani rahoton baya bayan nan da majalisar dinkin duniya ta fitar, ya nuna cewa ‘yan Venezuela miliyan 2 da dubu 300 ne suke rayuwa a wajen kasar, kuma miliyan daya da dubu 600 daga ciki, sun tsere daga kasar ne tun daga shekarar 2015.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI