Spain
Carles Puidgemont ya bukaci hanyar tattaunawa da Spain
Wallafawa ranar:
Tsohon Shugaban yan Awaren Catalonia dake gudun hijira, Carles Puigdemont ya bukaci kungiyar kasashen Turai da ta sanya baki domin sasanta rikicin yankin da gwamnatin Spain.
Talla
Yayin kaddamar da littafi kan rikicin a Brussels, Puigdemont ya bukaci shugaban kungiyar Turai Donald Tusk da ya taka rawa cikin matsalar.
A shekarar da ta gabata, Tusk yayi mumunar suka kan yadda gwamnatin Spain ke amfani da karfin da ya wuce kima kan masu zanga zangar goyan bayan ballewar yankin Catalonia.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu