Faransa

Bashi ya mamaye Faransa

A Faransa wani rahoto da hukumar kididiga ta fitar na nuni cewa bashin da ake bin Faransa na daf da zarce kasafin kudin kasar.Sakamakon daga hukumar INSEE na zuwa ne a wani lokaci da shugaban kasar Emmanuel Macron ke fuskantar koma baya wajen tafiyar da mulki.

Hukumar kididiga ta kasar Faransa
Hukumar kididiga ta kasar Faransa LOIC VENANCE / AFP
Talla

Rahotanni daga kasar ta Faransa na nuni da cewa bashin da ake biyar kasar na daf da cimma kasafin kudin kasar da kusan kashi dari bisa dari.

Bashin a cewar hukumar kididigar kasar ta Insee zai kai Euros tiriliyan 2 da bilyan 299, hakan baya ga bashin da ake bin kamfanin jiragen kasa na kasar SNCF kama da shekara ta 2016..

Wadannan alkalumma na zuwa ne ‘yan lokuta kadan bayan da babban bankin yankin Turai ke nazari domin don kara kudaden ruwa a basusuka da ta ke warewa kasashen yankin a lokacin bazara na shekara ta 2019.

Francois Escale tsohon alkalin kotun da ke mayar da hankali zuwa ga batutunwan da suka shafin tattalin arziki a Faransa ya yi kokarin duba halin da Jamus ke cikin kasancewar daddadiyar hulda da ke tsakanin kasashen biyu da cewa kasar ta Jamus ta samu ci gaba tare da magance da dama daga cikin wasu matsalloli kama daga bashi da suka mamaye ta ya yi da Faransa ke jan kafa, wanda zai iya kawo rashin jituwa tsakanin kasashen biyu dake kokarin cimma manufofi guda dangane da tarrayar Turai.

Tsohon alkalin ya yi sharhi tare da duba kujerar zaman wasu kasashen na Turai da yanzu haka suke fuskantar mantsi lamba daga babban bankin Turai kasancewar bashin da suke da shi ya zarce kasafin kudin kasar, irin su Italiya da kuma Girka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI