Isa ga babban shafi
Turai

Kasuwannin hannayen jarin Turai sun fadi

Kasuwannin hannayen jarin Turai sun fadi saboda kasafin kudin Italiya
Kasuwannin hannayen jarin Turai sun fadi saboda kasafin kudin Italiya Nicolas ASFOURI / AFP
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Hannayen jari a kasuwannin Turai sun fadi bayan da ‘yan kasuwan ke fargabar yadda Italiya ke tafiyar da kasafin kudinta, yayin da na Amurka ke ci gaba da tashi duk da yakin kasuwanci da ke ci gaba da kamari.

Talla

Fargabar da ta sake kunno kai sakamakon rikicin kasuwanci tsakanin Amurka da China, da kuma halin da siyasar Italiya ke ciki sun yi mummunar tasiri kan kasuwannin hannayen jari a Turai.

Masu zuba jarin sun kasance cikin fargaba game da yadda Italiyar ta tsara kasafin kudinta a wannan shekarar, in da gibin da ke cikin kudirin ya wuce yadda da dama suka yi tsammani, lamarin da ya ci karo da muradan Tarayyar Turai.

Shugaban Tarayyar Turai, Jean Claude Junker ya nuna rashin goyon bayansa karara ga matakin Italiya, in da yace, dole ne hukumarsa ta yi duk mai yiwuwa don kauce wa irin matsalar da aka samu a kasar Girka.

Italiya ta mayar da martani ta bakin mataimakin Firaminitanta, Matteo Salvini, wanda ya ce, za ta shigar da karar Tarayyar Turan saboda sukar da ta yi wa kasafin nata ya tsorata masu zuba jari.

Ya ce, rashin adalci ne Junker ya kwatanta kasarsa da Girka saboda haka a shirye Italiya take ta nemi a tilasta Tarayyar Turan ta biya ta diyya saboda wannan ta’adi na tattalin arziki da ta yi mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.