Faransa

Faransa zata sayar da manyan filayen jiragenta uku

'Yan majalisar dokokin Faransa sun kada kuri’a da gagarumin rinjaye kan kudurin shugaban kasar Emmanuel Macron na sayar da tashoshin jiragen saman birnin Paris uku, a wani bangare na shirin shugaban na samun karin kudade don biyan basuka.

Macron ya samu goyon bayan majalisar Faransa, kan kudurinsa na sayar da manyan filayen jiragen saman kasar uku.
Macron ya samu goyon bayan majalisar Faransa, kan kudurinsa na sayar da manyan filayen jiragen saman kasar uku. AFP/File
Talla

‘Yan majalisu 39 ne suka kada kuri’ar amincewa da kudurin, yayin da bakwai sukayi watsi da batun.

Tuni dai jam'iyyun adawa a kasar ta Faransa suka koka dangane da shirin gwamnatin na saida filayen jiragen na Charles de Gaulle, da Orly da kuma Le Bourget, dukkansu a birnin Paris, inda suka zargi gwamnati da sayar da kaddarori mafi mahimmanci ga kasar.

A halin da ake ciki gwamnatin Faransa na da kussan kashi 60 cikin dari, na hannu jari a tasoshin jiragen da suke a matakin manyan filin jiragen sama a duniya a girma da yawan jigilar fasinjoji.

Baya ga filin jiragen, ‘yan majalisun sun kuma amince da saida wani gidan cha-cha, bisa sharadin gwamnati zata rike kashi 20 cikin dari na hannun jarinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI