Turai

Italiya ta aike da yan Sanda zuwa iyaka da Faransa

Matteo Salvini,Ministan cikin gidan Italiya
Matteo Salvini,Ministan cikin gidan Italiya REUTERS/Remo Casilli

Ministan Italiya na cikin gida Matteo Salvini a jiya asabar ya aike da yan sanda zuwa kan iyaka da kasar Faransa don hana shigowar yan cin rani bayan da aka zargin jami`an tsaron Faransa da sauke wasu yan cin rani daf da kan iyaka da Italiya.

Talla

Daukar wannan mataki daga ministan cikin gidan Italiya na zuwa ne bayan fitar da wani bidiyo dake nuna yan sandan Faransa jibge wasu yan cin rani daf da kan iyaka da Italiya ,kafin daga bisali sun bada baya.

A wata zantawa da jaridar kasar ta Italiya, Matteo Salvini ya hakinkanta cewa suna da alkaluma dake nuna masu cewa kama daga watan janairun bana , Faransa ta dawo da yan cin rani 48.000 zuwa gabar ruwan Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.