Rasha-Amurka

Rasha ta gargadi Amurka kan ficewa daga yarjejeniyar makamai

Tun a shekarar 1987 shugaba Ronald Reagan ya sanya hannu kan yarjejeniyar wadda ke da nufin kayyade yawan muggan makaman da kowacce kasa za ta rika kerawa.
Tun a shekarar 1987 shugaba Ronald Reagan ya sanya hannu kan yarjejeniyar wadda ke da nufin kayyade yawan muggan makaman da kowacce kasa za ta rika kerawa. Alexander Zemlianichenko/Pool via REUTERS

Rasha ta yi gargadin cewa matakin da Donald Trump ya dauka na fitar da Amurka daga dadaddiyar yarjejeniyar nukiliyar da ke tsakaninsu bahaguwar dubara da bazata kai kasar ga ci ba.

Talla

A cewar mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkob ficewar Amurka daga yarjejeniyar wadda ke kayyade adadin makamain nukiliyar da kowacce kasa za ta rika kerawa a kowacce shekara na matsayin mafi munin ficewa daga yarjejeniya da Trump zai yi la’akari da yadda kai tsaye za ata iya shafar hatta tsaron daidaikun kasashe.

A cewar mataimakin ministan harkokin wajen na Rasha, ficewar Amurka daga yarjejeniyar zai haddasa yaduwar muggan makamai a sassan duniya wanda kuma ke barazana ga tsaron al’umma.

Ajiya asabar ne dai Donald Trump ya sanar da aniyarsa ta fitar da Amurka daga yarjejeniyar wadda ke kayyade adadin makaman da manyan kasashen ke kerawa.

Sergei Ryabkob ya yi ikirarin cewa matukar Amurkan ta tsaya kan bakanta na lallai sai ta fice daga yarjejeniyar babu shakka basu da zabi face suma su dauki matakan ramuwar gayya ciki kuwa harda fasahar soji.

Tun a shekarar 1987 shugaba Ronald Reagan ya sanya hannu kan yarjejeniyar wadda ke da nufin kayyade yawan makaman da kowacce kasa za ta rika kerawa kowacce shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.