Faransa-Sarkozy

Kotun daukaka kara a Faransa ta bukaci Sarkozy ya gurfana gabanta

Matukar dai kotu ta samu Sarkozy da laifukan da ake tuhumarsa tsohon shugaban zai shafe kusan shekara guda ko fiye a gidan kaso.
Matukar dai kotu ta samu Sarkozy da laifukan da ake tuhumarsa tsohon shugaban zai shafe kusan shekara guda ko fiye a gidan kaso. REUTERS/Gonzalo Fuentes

Kotun daukaka kara a Faransa ta bukaci tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy ya bayyana gabanta don amsa tuhume-tuhume masu alaka da kashe kudaden da suka zarta kima a yakin neman zaben sa na 2012 da bai yi nasara ba.

Talla

Hukuncin kotun na yau ya bukaci tsohon shugaban na Faransa Nicolas Sarkozy ya gurfana gabanta kan zargin na kashe yuro miliyan 43 a zaben 2012 da ya sha kaye, ko da dai tsohon shugaban mai shekaru 63 ya sha alwashin daukaka kara wanda zai zamo na karshe a karakin da ya dau lokaci yana daukakawa.

Kusan dai za a iya cewa wannan tuhuma na daga cikin tuhume-tuhume da suka yi wa Sarkozy katutu tun bayan saukarsa daga madafun iko, wanda ya ke ci gaba da musanta zargin tsawon lokaci.

Matukar dai kotu ta samu Sarkozy da laifukan da ake tuhumarsa tsohon shugaban zai shafe kusan shekara guda ko fiye a gidan kaso.

Sarkozy wanda ya jagoranci Faransa daga 2007 har zuwa 2012 kafin rasa madafun iko a hannun Francoise Hollande a 2012 shi ne shugaban Faransa na 3 da ake tuhuma da laifukan cin hanci da rashawa.

Baya ga zargin na kashe kudin da suka wuce kima a 2012 akwai kuma tuhumar karbar wasu makudan kudi daga hannun tsohon shugaban Libya Mu’ammar Gaddafi don gudanar da yakin neman zabensa karon farko a 2007.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.