NATO-Rasha

Kungiyar tsaro ta NATO ta fara atisaye mafi girma a tarihi

Sai dai tuni Rasha ta yi kakkausar suka ga salon atisayen wanda ta bayyana da yunkurin kalubalantarta.
Sai dai tuni Rasha ta yi kakkausar suka ga salon atisayen wanda ta bayyana da yunkurin kalubalantarta. REUTERS/Ahmad Nadeem

Kungiyar tsaro ta NATO ta fara wani atisayen soji mafi girma a tarihi tun bayan kawo karshen yakin cacar baka wanda ya kunshi sojoji fiye da dubu hamsin. Sai dai tuni Rasha ta kira atisayen da wanda aka shirya da gan-gan don nuna adawa da ita.

Talla

Atisayen sojin wanda ke gudana a Norway ya kunshi Sojoji fiye da dubu 50 sai motocin yaki dubu 10 da jiragen ruwa na yaki 65 kana da jiragen yaki 250 dukkaninsu daga kasashe mambobin kungiyar 31.

An dai yi ittifakin atisayen shi ne irinsa mafi girma da NATO ta taba gudanarwa a tarihi tun bayan kawo karshen yakin cacar baka, ko da dai sakater Janar na kungiyar Jens Stoltenberg ya ce daukar matakin atisayen ya zama wajibi la’akari da barazanar tsaron da nahiyar Turai ke fuskanta.

Sai dai tuni Rasha ta yi kakkausar suka ga salon atisayen wanda ta bayyana da yunkurin kalubalantarta la’akari da yadda ake gudanar da shi a makociyarta da su ka hada kan iyaka mai tazarar kilomita 198 daga arewaci.

Ofishin jakadancin Rasha da ke Oslo ya ce Rashan ta tsaya a zukatan kasashen yamma wanda ita kuma ko kadan basa gabanta.

Ko a watan Satumba ma Rashan ta gudanar da wani atisayen Soji mafi girma bayan da ta kwace iko da yankin Crimea ta kuma karfafa ayyukan sojinta a yankin.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Rasha Maria Zakharova ya ce takalar fada ke sanya kasashen na yammaci kara yawan sojinsu a Norway don barazana ga Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.