Faransa

Wasu kasashen turai tara, na taron nazarta kafa rundunar tsaronsu a Paris

shugaban Faransa Emanuel Macron
shugaban Faransa Emanuel Macron AFP

A yau laraba ne, wakilan wasu  kasashen  tarayyar Turai guda 9 da suka sanya hanun amincewa da samar da rundunar tsaro a nahiyar, sun fara gudanar da wani taro a birnin Paris na Faranasa. Domin nazarta shawarar da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gabatar, ta son kasashen su samar da wata rundunar tsaro  ta musamman, domin tunkarar barazana  daga kasashen Rasha da China, tare da  rage dogaro da suke yi da Amurka wajen  sumun tsaro.

Talla

Shugaba Macron ya yi wannan kiran ne a dai dai lokacin da ake bikin cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na farko, kuma tun darewarsa kan karagar mulki ya bukaci kafa wannan runduna don rage dogaro da Amurka, wadda shugabanta Donald Trump ya ce, zai janye kasar daga yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma da ita bayan yakin cacar baka.

Macron ya ce, a lokacin da shugaba Trump ke sanar da wannan aniya tasa ta fice daga gagarumar yarjejeniyar wadda aka cimma bayan kawo karshen rikicin makamai masu linzami a shekarun 1980 a Turai, babu abin da ya zo masa a rai illa tunawa da halin da nahiyar ta tsinci kanta a ciki a wancan lokaci.

Shugaban na Faransa ya ce, ba za a su iya bai wa kasashen Turai kariya ba har sai sun kafa wannan runduna.

Shugaba Macron dai, shi ne wanda ya jagoranci kafa wata runduna tsakanin kasashen Turai 9, da za ta rika bada agajin ggaggawa musamman a lokacin aukuwar bala’oi tare da kwashe jama’a daga yankin da yaki ya afka masa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.