London

Kungiyar kare hakkin 'yan Jaridu na taronta karon farko a London

Taron na wannan karon zai fi mayar da hankalin kan kisan gillar baya-bayan nan da aka yiwa dan jaridar Saudiya Jamal Khashoggi.
Taron na wannan karon zai fi mayar da hankalin kan kisan gillar baya-bayan nan da aka yiwa dan jaridar Saudiya Jamal Khashoggi. rsf.org

Kungiyar kare hakkin 'Yan Jaridu ta Duniya, Reporters Without Borders, a karon farko ta kai bikin karramar Yan Jaridun da ta ke yi kowacce shekara birnin London, wanda ya mayar da hankali kan bukatar kare 'Yan Jaridun daga munanan hare haren da su ke fuskanta.

Talla

Kungiyar ta ce akalla 'Yan Jaridu 63 aka kashe bana, tare da wasu masu ba da bayanai 11 da masu taimakawa 'Yan Jaridu 4, kuma cikin wadanda aka kashe har da Dan Jaridar Saudiyya, Jamal Khashoggi.

Wannan adadi ya zarce na shekarar bara wanda ya nuna cewar Yan Jaridu 55 aka kashe.

Cikin wadanda suka taba lashe kyautar kungiyar sun hada da Liu Xiabo daga China da Raif Badawi daga saudiyya da Jaridar Cumhuriyat daga Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.