Isa ga babban shafi
Faransa-Amurka

Macron da Trump sun gana a Paris

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin karbar bakuncin Donald Trump a birnin Paris.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin karbar bakuncin Donald Trump a birnin Paris. Vincent Kessler/REUTERS
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayi yunkurin kawo karshen sabuwar takkadamar da ta kunno kai tsakaninsa da shugaba Donald Trump na Amurka, dangane da batun samar da rundunar dakarun kasashen turai.

Talla

Macron ya yi wannan kokari ne yayin wata ganawa da shugabannin biyu suka yi a yau Asabar a birnin Paris duk da tsamin dangantakar dake tsakaninsu, inda shugabannin kasashe ke halartar taron bikin cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na daya.

A baya bayan nan ne shugaba Trump yayi amfani da shafinsa na twitter wajen caccakar takwaransa na Faransa, dangane da shawarar da ya bayar na bukatar kafa runduna ta musamman da zata kunshi dakarun kasashen turai zalla, abinda Trump ya bayyana da gurguwar shawara idan aka yi la’akari da yadda kungiyar kasashen turai EU ta kasa bada kaso mai tsoka ga rundunar tsaro ta NATO, a cewar shugaban na Amurka.

Trump ya kuma bayyana rashin jin dadin yadda Macron ya bayyana cewa kafa rundunar na da muhimmanci domin baiwa kasashen turai kariya daga yiwuwar kai musu farmaki daga kasashe irinsu Amurka, China da kuma Rasha.

Sai dai yayin shirye-shiryen bude bikin na yau, shugabannin biyu sun gana cikin raha, inda shugaba Macron ya bayyana jin dadinsa dangane da hadin kan dake tsakanin Faransa da Amurka duk da banbancin dake tsakaninsu a wasu fuskoki na Diflomasiya.

Shugabannin kasashen duniya akalla 70 ne ke halartar taron bikin cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na 1, wanda za’a soma shi a wannan Lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.