Tawagar 'yan gudun hijira ta ci gaba da tunkarar Amurka
Wallafawa ranar:
Tawagar ‘yan gudun hijirar da ta taso daga kasar Honduras mai kunshe da akalla mutane dubu 500, ta ci gaba da tafiya domin isa Amurka.
A ranar Asabar tawagar ‘yan gudun hijirar ta bar birnin Mexico City inda ta durfafi yankin arewaci don isa kan iyakar Mexico da Amurka.
Cigaba da tattakin ‘yan gudun hijirar ya zo ne ne kwana guda bayan dokar da shugaban Amurka Donald Trump ya sanyawa hannu, wadda ta dakatar da baiwa bakin-haure ko ‘yan gudun hijirar damar shiga Amurka har na tsawon kwanaki 90.
Shugaban na Amurka ya kuma tura sojoji akalla dubu 5 zuwa kan iyakar Amurkan da Mexico da nufin dakile duk wani yunkurin 'yan gudun hijirar na shiga cikin kasar.
A ranar 13 ga watan Oktoba wannan gagarumar tawaga ta ‘yan gudun hijira suka bar birnin san Pedro Sula na kasar Honduras domin isa Amurka, kuma zuwa yanzu, sun shafe tafiyar sama da nisan kilomita dubu 1, 500.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu