Birtaniya-EU

May na neman amincewar Majalisar Birtaniya kan Brexit

Firaministar Birtaniya Theresa May
Firaministar Birtaniya Theresa May REUTERS/Toby Melville

Firaministar Birtaniya, Theresa May na kokarin shawo kan Majalisar Dokokin Kasar don ganin ta amince da yarjejeniyar ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan Uwargida May ta samu goyon bayan Majalisar Ministocinta kan shirin kasar na ficewar duk da cewa tana fuskantar turjiya daga Jam’iyyarta ta Democratic Unionist.

Bayan kwashe sa’oi 5 ana tafka mahawara, May ta shaida wa manema labarai cewar sun cimma matsaya a Majalisar Ministocin, kuma yanzu abin da ya rage shi ne samun amincewar Majalisar Dokoki.

Ana saran nan ba da jimawa ba, Jam’iyyar Labour mai adawa ta sanar da matsayinta na nuna goyon baya ko akasin haka ga yarjejeniyar, yayin da shugabanta, Jeremy Corbyn ya ce, bai yi amanna cewa, yarjejeniyar mai shafuka 585, ta yi dai dai da muradun Birtaniya ba.

A safiyar ranar Alhamis ne, Uwargida May za ta gabatar da wata sanarwa ga Majalisar Wakilan Kasar wadda ke da alhakin amincewa da yarjejeniyar kafin ficewar kasar baki daya daga EU a ranar 29 ga watan Maris.

A bangare guda, shugaban Majalisar Tarayyar Turai, Donald Tusk zai zartas da hukuncinsa kan yarjejeniyar a birnin Brussels, yayin da gwamnatin Birtaniya ke fatan ganawa da shi a cikin wannan wata don kammala cimma yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.