EU-Birtaniya

Ministocin May 4 sun yi murabus kan shirin ficewar kasar daga EU

May dai yanzu haka na fuskantar matsin lamba hatta daga mambobin jam'iyyarta kan shirin ficewar a dai dai lokacin da ta gaza cimma yarjejeniya da EU duk da karatowar lokacin ficewar.
May dai yanzu haka na fuskantar matsin lamba hatta daga mambobin jam'iyyarta kan shirin ficewar a dai dai lokacin da ta gaza cimma yarjejeniya da EU duk da karatowar lokacin ficewar. Reuters

Firaministar Birtaniya Theresa May na ci gaba da fafutukar ganin ta samu rinjaye kan mambobin Majalisar kasar a shirinta na fitar da Birtaniyar daga Kungiyar Tarayyar Turai a dai dai lokacin da wasu karin ministoci ke ci gaba da ajje mukaminsu tare da kalubalantar shirin a bangare guda kuma masu adawa da shirin ficewar ke neman a kadawa Firaministar kuri’ar yankan kauna.

Talla

Firaminista Theresa May ta kara fuskantar mafi munin kalubale ne a majalisar ministocinta bayan murabus din hudu a yau din nan baya ga sakataren shirin ficewar Dominic Raab wadanda dukkaninsu yanzu suka dawo kalubalantar matakin na ta na ficewa daga EU.

Bangarorin da ke adawa da shirin ficewar Birtaniyar daga EU na ganin dai dole ko dai ta samu cimma cikakkiyar yarjejeniya da kungiyar ta EU gabanin kammala ficewarta a ranar 29 ga watan Maris na shekara mai kamawa ko kuma kasar ta hakura da batun ficewar dungurugum.

Tuni dai jagoran masu adawa da shirin na May, daga Jam’iyyar Conservative Jacob Rees-Mogg ya mikawa majalisar kasar wata wasika da ke neman sahale musu kadawa Firaministar kuri’ar yankan kauna.

Kawo yanzu dai makamancin wasikar neman kadawa Firaminstar kuri’ar yankan kauna guda 48 ne suka isa gaban Majalisar ciki har da wasu daga Jam’iyyar da ta ke ciki ta Democratic Unionist.

Sai dai a kalamanta na yau din nan Theresa May ta ce ta na aiwatar da komi don ci gaban Birtaniya da Al’ummarta kuma tana fatan samun nasara kan kudirin da ta sanya a gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.