faransa

An Saki fitaccen Malamin Islama na Faransa Tariq Ramadan daga gidan kaso

Tariq Ramadan  a Nantes a shekara ta 2010
Tariq Ramadan a Nantes a shekara ta 2010 rfi

Hukumomi a kasar Faransa sun saki fitaccen Malamin Islaman nan Tariq Ramadan daga gidan kaso, bayan tsare shi tun watan biyu na wannan shekara bisa zargin yiwa wasu mata biyu fyade a wasu lokutta chan baya.

Talla

A jiya Juma'a aka bada shi beli bayan da ya bada tabbacin cewa bashi da wani abin fargaba.

Dan shekaru 56, masani dan asalin kasar Switzerland da yak e hutu daga jami'ar Oxford inda yake koyarwa, ya musanta dukkan zargin da ake masa na yiwa wata nakasasshiya fyade a shekara ta 2009, da kuma wata macce ta biyu a shekara ta 2012.

Karkashin belin nasa da aka bayar zai ajiye jingine kudi da suka kai Euro dubu 300, sannan kuma ya ajiye takardan sa na fasfo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.