Faransa-Zanga-Zanga

Fiye da masu zanga-zanga 400 sun jikkata a Faransa

Dubban mahalarta zanga-zangar ta yau kenan sanye da riguna masu launin dorawa alamun kayan direbobin Tasi a Faransar inda su ke nuna adawarsu da shirin kara farashin man na Fetur.
Dubban mahalarta zanga-zangar ta yau kenan sanye da riguna masu launin dorawa alamun kayan direbobin Tasi a Faransar inda su ke nuna adawarsu da shirin kara farashin man na Fetur. REUTERS/Charles Platiau

Sama da mutane 400 suka jikkata, in da 14 daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali biyo bayan zanga-zangar da Faransawa suka gudanar don nuna rashin amincewarsu da matakin gwamnatin kasar na karin farashin man fetir.

Talla

Ministan Cikin Gidan Faransa, Christophe Castaner ya tabbatar da alkaluman wadanda suka jkkata sakamakon zanga-zangar wadda ta yi sanadin ajalin mutun guda.

Ministan Cikin Gidan ya bayyana zanga-zangar da aka gudanar wurare 87 a sassan Faransa a matsayin tashin hankali, yayin da jami’an ‘yan sanda da masu kashe gobara ke cikin wadanda suka samu rauni.

Masu boren sanye da riguna masu launin dorawa, sun rufe hanyoyin zirga-zirga, abin da ya haddasa cinkoson ababan hawa duk da dai a baya-bayan an samu rahotannin da ke cewa, zanga-zangar ta fara sauki.

Akalla mutane dubu 288 ne suka amsa kiran shiga wannan gagarumar zanga-zangar kamar yadda Ministan Cikin Gidan kasaar ya tabbatar a wata hira da aka yi da shi a karshen mako, yayin da jami'an tsaro suka kama 157 daga cikinsu.

A cewar Ministan, masu zanga-zangar sun yi ta dirkar barasa, abin da ya alakanta da musabbabin aukuwar fadace-fadace da soke-soke a tsakaninu.

Faransa ta ce, tana da masaniya game da rashin jin dadin al’umma na karin farashin man, amma wani mataki ne da ya zame mata dole ta dauka don kawo sauyi a fannin tattali arziknta da zummar rage dogaro da man na fetir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.