Jamus-Saudiya

Jamus ta sanyawa wasu 'yan Saudiya 18 takunkumi kan kisan Khashoggi

Ba tun yanzu ba dai Jamus ke nuna rashin amincewarta kan bayanan da Saudiya ke bayarwa game da kisan dan jaridar Jamal Khashoggi.
Ba tun yanzu ba dai Jamus ke nuna rashin amincewarta kan bayanan da Saudiya ke bayarwa game da kisan dan jaridar Jamal Khashoggi. Fuente: Reuters.

Jamus ta sanar da takunkumai a kan wasu ‘yan kasar Saudiyya 18 da ake zargin da hannu wajen kashe dan Jarida Jamal Khashoggi a Ofishin jakadancin Saudin da ke birnin Santambul na Turkiya ranar 2 ga watan Oktoba.

Talla

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas, ya ce karkashin wannan mataki, za a hana mutanen 18 iznin samun visar Schengen da ke bayar da damar shiga yankin Turai.

Haka zalika tuni Jamus da gindaya sharuddan dai na sayarwa Saudiyan makamai baya ga soke cinikin makaman da suka cimma tsakaninsu a baya-bayan nan.

Saudiyar dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga kasashen Turai tun bayan binciken baya-bayan nan da ke nuna cewa da hannun yarima mai jiran gado na kasar Muhammad Bin Salman dumu-dumu a umarnin kisan dan jaridar Jamal Khashoggi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.