Faransa

Zanga-zangar lumana daga kungiyar Yellow West a Paris

Taron masu zanga-zanga a Paris na kasar Faransa
Taron masu zanga-zanga a Paris na kasar Faransa REUTERS/Benoit Tessier

A Faransa,bayan share kusan mako daya suna gudanar da zanga –zanga,kungiyar masu sanye da riguna masu ruwa kwai,Yellow West saboda nuna adawar su da tsadan mai a kasar sun dau alkawali na ci gaba da zanga-zangar duk da matakan tsaro da hukumomin kasar suka dau.

Talla

Kungiyar na samun goyan bayan da dama daga cikin masu adawa da manufofin Shugaban kasar Emmanuel Macron ta sanar da gudanar da wannan zanga-zanga a birnin Paris a yau asabar.

Hukumomin birnin Paris sun amince tareda bayar da izinin gudanar da zanga-zangar lumana tareda baiwa kungiyoyin izinin gudanar da taron su a wurin shakatawa dake filin Champs Elysee, bukatar da kungiyoyin suka yi watsi da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.