Amurka

Jami'an kwana-kwana sun yi nasarar kashe gobarar dajin California

Daya daga cikin yankunan da gobarar daji ta yi barna a jihar California.
Daya daga cikin yankunan da gobarar daji ta yi barna a jihar California. REUTERS/Terray Sylvester

Hukumomin Amurka sun bayyana nasarar kashe wutar dajin da aka samu a California wadda ta kwashe sama da makwanni biyu tana ci ba tare da kaukautawa ba.

Talla

Wutar dajin da ta fara ci tun ranar 8 ga wannan wata, tayi sanadin hallakar mutane 87, yayin da 249 suka bata.

Alkaluman da hukumomin kasar suka bayar sun nuna cewa, wutar ta lashe fadin kada da ya haura eka dubu 153, zalika gobarar ta kone gidaje kusan dubu 14, da wasu gine gine na daban.

Jami’an sun ce ruwan saman da aka samu mai karfi ya taimaka gaya wajen kashe wutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.