Turai

Theresa May ta mayarwa Trump da martani

Teresa May, Firaministar Birtaniya
Teresa May, Firaministar Birtaniya REUTERS/Dylan Martinez

Firaministar Birtaniya Theresa May ta caccaki shugaba Donald Trump kan sukar da ya yiwa yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar kasashen Turai na ficewar ta daga kungiyar.Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da zata kai ziyara Wales da Ireland ta Arewa domin samun goyan bayan su.

Talla

Faraministar Theresa May ta mayarwa Shugaban Amurka Donald Trump da martani ne a lokacin da take cikin kai ziyara a yankin Wales, ziyar da take a cikin Birtaniya domin tallata yarjejeniyar da aka samu tsakanin kasar da tarayyar Turai, wadda kuma yan majalisa masu zazzafan ra’ayi na iya fatali da ita a zaman majalisar na ranar 11 ga watan Disamba mai kamawa.

A cikin furucin da Trump yayi kan yarjejeniyar, shugaban Amurka ya bayyana cewa, yarjejeniya tana da kyau ga tarayyar Turai, amma za ta kawo cikas ga kasuwanci tsakanin Amurka da Birtaniya, don haka sai sun natsu tareda duba ko Birtaniyar na da yancin gudanar da kasuwancin. .Trump ya kara da cewa, idan aka duba yarjejeniyar, akwai ayar tambaya dangane yiyuwar gudanar da kasuwanci tsakannin Birtaniya da Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.