Amurka

Tsohon shugaban Amurka George Bush ya mutu

Tsohon shugaban Amurka na 41, George H.W. Bush wanda ya rasu a ranar Juma'a yana da shekaru 94.
Tsohon shugaban Amurka na 41, George H.W. Bush wanda ya rasu a ranar Juma'a yana da shekaru 94. REUTERS/Donna Carson/File Photo

Shugabanni kasashen duniya da kuma wakilansu na ci gaba da mika sakon taya alhini ga iyalan tsohon shugaban Amurka George Bush, wanda ya rasu ranar Juma'a yana da shekaru 94.

Talla

George Bush ya jagoranci Amurka tsawon wa’adi guda daga shekarar 1989 zuwa 1993, a matsayin shugaban Amurka na 41.

Goerge Bush mahaifi ne ga tsohon shugaban Amurka Goerge W Bush shugaban kasar na 43.

Za’a rika tuna gwamnatin tsohon shugaban na Amurka da rawar da ta taka wajen kafa makekiyar rundunar sojin kasar mai karfin dakaru dubu 400,000 da kuma hadakar karin wasu dakarun na kawayenta, domin fatattakar sojojin Iraqi a karkashin gwamnatin marigayi Saddam Hussien da suka mamaye kasar Kuwaiti a waccan lokacin.

An dai haifi Goerge H.W. Bush a ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1924, kuma mahaifansa sune Sanata Prescott Bush da Dorothy Bush.

Tsohon shugaban Amurkan na 41, ya zama matukin jirgin yaki mafi karancin shekaru a tarihin kasar yana da shekaru 18 kacal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI