Birtaniya

'Yan majalisa sun zargi Fira Ministar Birtaniya da yaudara

Fira Ministar Birtaniya Theresa May.
Fira Ministar Birtaniya Theresa May. REUTERS/Kevin Coombs

Wasu ‘yan majalisar Birtaniya sun zargi Fira Ministan kasar Theresa May da yaudara wajen sakaya wasu ginshikan yarjejeniyar ficewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai.

Talla

Zargin na zuwa ne wata guda bayanda Theresa May da wakilcin kungiyar ta EU suka sanya hannu kan yarjejeniyar rabuwar a Brussels.

Ian Blackford na jam’iyyar adawa ta SNP ne ya jagorancin ‘yan majalisar dake zargin Fira Ministan da yin rufa-rufa dangane da wasu batutuwan da yarjejeniyar ta kunsa.

Mafi muhimmanci daga cikin batutuwan da 'yan majalisar ke zargin May da yin rufa rufa akai shi ne batun yankin kasar na arewacin Ireland da aka barshi a karkashin dokokin bai daya na hukumar kwastam din tarayyar turai, matakin da zai tilastawa Birtaniyar bin wasu dokokin tattalin arzikin kungiyar ta EU nan da wasu shekaru bayan ficewarta a watan Maris na 2019.

Sai dai Theresa May ta musanta zargin inda ta ce, har zuwa lokacin da aka sanya hannu kan yarjejeniyar ta karshe bata taba yin rufa-rufa kan kalubalen da za su fuskanta bayan raba gari da EU ba.

‘Yan majalisar kasar ta Birtaniya da dama ne ke neman Fira Minista Theresa May ta koma birnin Brussels domin sake sabuwar tattaunawa da Wakilan EU dangane da yiwa yarjejeniyar rabuwar da suka cimma kwaskwarima. Sai dai tuni shugabancin kungiyar ta EU ya jadada cewa ba zai sake bude kofar yiwa yarjejeniyar kwaskwarima ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.