Faransa

Zanga-Zanga Faransa ta haifar da cikas ga tattalin arzikin

Yan Sanda a kokarinsu na dakile zanga-zanga a Faransa
Yan Sanda a kokarinsu na dakile zanga-zanga a Faransa REUTERS/Stephane Mahe/

Zanga zangar nuna rashin amincewa da harajin makamashin man feutr da wutar lantarki da masu sanye da riguna kalar dorowa suka share tsawon makwanni uku suna yi a Faransa, ta haifar da manyan illoli, da wasun su, za su bar daddadiyar alama ga kasar.

Talla

Illolin sun hada ne da tsinkewar ziyarar baki masu yawon bude ido da kuma tsayawar harakokin tattalin arziki, kone konen motoci da kuma kwasar ganima da aka gudanar a ranar asabar da ta gabata a birnin Paris.

Hotunan zanga zangar da suka zagaye duniya ta shafukan intanet abinda ya zubar da mutuncin kasar kamar yadda Jean-Virgile Cance, shugaban gungun masu gidajen Otel na kasar Faransa ya sanar.

Tuni dai tanadin dakunan Otel da ake yi a irin wannan lokaci na shagulgulan sabuwar shekara ya sauka kasa da kimanin kashi 10 zuwa 15% a shekara,

A cewar Jean-Virgile Cance datse hanyoyin mota da rufe hanyoyin shiga wasu wurarren ajiyar man da masu zanga zangar suka yi a ko ina cikin fadin kasar ta Faransa .

Sai dai kuma anasa bangaren masani tattalin arziki Mathieu Plane yace duk da zanga zagar, tattalin arzikin na Faransa na numfashi, sai dai idan an ci gaba da zanga zangar zai iya cintar kansa cikin mawuyacin hali.

Shugabam Faransa Emmanuel Macron zai yi jawabi zuwa yan kasar don kwantar da hankulan masu tarzoma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI