Belgium

Yan Sanda na tsare da masu zanga-zanga 400 a Belgium

Taron masu zanga-zanga a Bruxos na kasar Belguim
Taron masu zanga-zanga a Bruxos na kasar Belguim REUTERS / Yves Herman

A Belgium akalla mutane 400 ne yan Sanda suka capke bayan wata tarzoma da ta kuno kai a lokacin wata zanga-zanga da aka gudanar a birnin Bruxos.

Talla

Masu zanga-zanga dake sanye da riguna masu kalar dorowa sun datse wasu manyan hanyoyin birnin tareda bukatar ganin gwamnatin kasar ta soke wasu daga cikin matakan da ta dau, daga cikin bukatun su akwai batun kyautata rayuwar al’umat.

Gwamnatin kasar na fatan shiga tattaunawa da kungiyoyin kwadago domin warware wannan matsalla a kasar ta Belgium.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI