Faransa

Macron ya nemi afuwar Faransawa bisa harzuka su da ya yi

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin gabatar da jawabi ga 'yan kasar kan zanga-zangar adawa da gwamnati a birnin Paris. 10/12/2018.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayin gabatar da jawabi ga 'yan kasar kan zanga-zangar adawa da gwamnati a birnin Paris. 10/12/2018. Yoan Valat/Pool via REUTERS

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya baiwa al’ummar kasar hakuri kan wasu kalaman sa da yace sun harzuka jama’a zuwa yin zanga-zangar da ta juye zuwa tarzoma.

Talla

Wannan ya biyo bayan kazamar zanga zangar da aka kwashe kwanaki ana yi wadda ta haifar da asarar dukiya da jukkata jama’a a sasan kasar musamman ma a birnin Paris.

Yayin jawabin nasa, Macron ya kuma bayyana shirin karin albashi ga ma’aikata, wanda ya ce daga farkon shekarar 2019 mai zuwa, gwamnati za ta yiwa ma’aikata karin euro 100 bisa albashinsu ba kuma tare da biyan haraji.

Shugaban ya kara da cewa daga sabuwar shekarar za kuma a rika biyan kudaden karin lokacin aiki, ba tare sanya musu haraji ba.

Kari kan tagomashin da gwamnatin ta Faransa ta alkawartawa ‘yan kasa sun hada da janye haraji daga kan kudaden karshen shekara da za’a biya ma’aikata da kuma kudaden ‘yan fansho.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI