Faransa-Strasbourg

Jami'an tsaron Faransa sun nemi dauki a farautar maharin Strasbourg

Rahotanni sun ce a yau adadin Jami'an tsaron da ke laluben maharin na Strasbourg ya kai 720 yayinda kawo yanzu aka gaza gano shi.
Rahotanni sun ce a yau adadin Jami'an tsaron da ke laluben maharin na Strasbourg ya kai 720 yayinda kawo yanzu aka gaza gano shi. REUTERS/Vincent Kessler

Jami’an ‘yan sandan Faransa sun nemi dauki a rangadin da su ke don farautar maharin kasuwar Kirsimeti ta birnin Strasbourg Cherif Chekatt wanda ya hallaka mutane 4 baya ga jikkata wasu karin 12.

Talla

Tuni dai aka kara yawan jami’an tsaro kan adadin dari 600 da aka baza a jiya kan iyakar Faransa da Jamus don kamo Cherif mai shekaru 29 da ya shafe tsawon lokaci ya na zaman yari a Jamus kan laifukan fashi da makami.

Rahotanni sun ce bayan zaman Cherif na tsawon lokaci a gidajen yari daban daban ne ya samu tsattsaurar akidar addini wadda ta kai shi ga kai harin, ko da dai kawo yanzu ba su bayyana harin da na ta'addanci ba.

Tuni dai gwamnatin Faransa ta nemi tsagaita zanga-zangar kasar bayan harin wanda ta ce maharin ka iya fakewa da ita wajen hallaka tarin jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI