Birtaniya

Birtaniya ta bayyana tsarin shige da ficenta bayan Brexit

Fira Minista Theresa May ta sha alwashin sauya tsarin shige da ficen Birtaniya bayan kammala fita daga EU.
Fira Minista Theresa May ta sha alwashin sauya tsarin shige da ficen Birtaniya bayan kammala fita daga EU. AFP

Birtaniya ta bayyana wasu kudurori na rage yawan mutanen da za su rika shiga kasar daga sauran kasashen Turai bayan kammala ficewarta daga kungiyar kasashen ta EU, a shekarar 2019.

Talla

Matakin ya zo ne yayin da masana ke gargadin cewa, tattalin arzikin kasar, ba zai iya jurewa rabuwarta da EU ba tare da kulla yarjejeniya ba.

Wasu daga cikin sabbin kudurorin fayyace tsarin shige da ficen sauran ‘yan kasashen turai a Birtaniyar sun kunshi, bada takardar izinin shiga kasar ta wucin gadi ga ma’aikata baki, wanda a karkashin hakan ma’aikatan ba su da damar kawo iyalansu kusa, zalika ba su da hurumin neman zaman kasar na din-dn-din.

Ba tun yau ba dai, Fira Ministan Birtaniya Theresa May, ta sha alwashin kawo karshen abinda ta kira sakakken ‘yancin da sauran ‘yan kasashen nahiyar turai ke amfana da shi na shige da fice a kasar ba tare da shamaki ba, abinda ta ce yana daya daga cikin dalilan da ya sanya al’ummar kasar suka kada kuri’ar rabar gardama ta ficewa daga kungiyar ta EU a 2016.

Tun bayan zaben rabar gardamar na 2016, an samu raguwar dubban mutane daga sauran kasashen Turai da ke shiga Birtaniya, inda sakamakon wata kididdiga ya nuna cewa a shekarun 2014 da 2015 sama da mutane dubu 300 ne daga sassan turai suka shiga kasar, to amma a shekarar 2017, sun ragu zuwa dubu 280.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.