Amurka

Kashi daya bisa hudu na ayyukan gwamnatin Amurka sun tsaya

Matakin dakatar da wasu ayyukan gwamnatin Amurka zai ci gaba da wanzuwa har zuwa bayan bikin Kirsimeti.
Matakin dakatar da wasu ayyukan gwamnatin Amurka zai ci gaba da wanzuwa har zuwa bayan bikin Kirsimeti. AFP

Bayanai daga Amurka sun ce matakin dakatar da wasu ayyukan gwamnatin Amurka ka iya ci gaba da wanzuwa har zuwa bayan bikin Kirsimeti.

Talla

Za a fuskanci tsaikon a Amurka ne a dalilin gaza cimma matsaya da ‘yan majalisar dokokin kasar a zaman da suka sake yi a jiya Asabar, kan amincewa da bukatar shugaba Donald Trump, da ke neman Dala biliyan 5.7 don gina katafariyar ganuwa akan iyakar kasar da Mexico.

Rahotanni sun ce a halin yanzu, kashi 1 bisa 4 na ayyukan ma’aikatun gwamnatin Amurka sun tsaya cak sakamakon matakin gwamnati na kin ba su kudade, har sai majalisar ta amince da bukatar Trump.

A ranar 27 ga watan Disamba ake sa ran ‘yan majalisar za su sake zama kan bukatar domin kada kuri’a.

A farkon watan Nuwamba shugaba Donald Trump ya rattaba hannu kan wata doka da ta dakatar da shigar ‘yan gudun hijira cikin Amurka daga kan iyakar ta da Mexico na tsawon kwanaki 90.

Zalika shugaban ya kuma aike da sojoji akalla 5,000 a kan iyakar Amurkan da Mexico, domin hana tawagar ‘yan gudun hijira mai dauke da kimanin mutane 7000 shiga Amurka, wadanda suka taso daga kasashen nahiyar kudanci da tsakiyar Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI