Faransa-Rwanda

Faransa ta dakatar da binciken harin 1994 a Rwanda

Harin watan Aprilun 1994 da ya kai ga hallakar Juvenal Habyarimana tsohon shugaban kasar Rwanda.
Harin watan Aprilun 1994 da ya kai ga hallakar Juvenal Habyarimana tsohon shugaban kasar Rwanda. Reuters

Alkalan Faransa sun dakatar da binciken da suka kwashe tsawon lokaci su na gudanarwa kan harin da aka kai wa marigayi tsohon shugaban Rwanda, Juvenal Habyarimana a shekarar 1994, abin da ya haddasa kisan kare dangi a kasar.

Talla

A watan Aprilun 1994 ne wasu da kawo yanzu ba a kai ga gano ko su waye ba, suka harbo jirgin tsohon shugaban kasar ta Rwanda Juvenal Habyrimana batun da ya yi sanadin mutuwarsa baya ga haddasa rikicin kwanaki 100 da ya kai ga asarar rayuka kimanin dubu dari takwas.

Binciken dai ya kasance ummul-haba’isin rashin jituwa tsakanin Faransa da Rwanda bayan tuhumar da aka yi wa wasu mutane bakwai makusantan shugaban kasar mai ci, Paul Kagame.

Ko a cikin watan Oktoban da ya gabata, sai da masu shigar da kara a Faransar suka bukaci kawo karshen binciken saboda rashin kwararan shaidu kan mutanen bakwai.

Tuni dai bangaren masu shigar da kara suka sha alwashin daukaka kara don lalubo tare da hukunta masu hannu a kisan tsohon shugaban.

Cikin tsawon shekaru da aka dauka ana wannan bincike, rahotanni sun ce gwamnatin Rwanda ba ta taba bayar da taimako wajen ganin an lalubo masu hannu a kisan da kuma haddasa rikicin ba, yayinda ta ke zargin Faransa da rura wutar rikicin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI