Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine

An soma tattaunawar sulhunta rikicin gabashin Ukraine

Wasu sojin kasar Unkraine a yankin Donetsk.
Wasu sojin kasar Unkraine a yankin Donetsk. AFP/Anatolii Stepanov
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Yau Asabar wakilan kasashen Ukraine da Rasha, da kuma na kungiyar Tarayyar Turai EU ke ganawa domin kawo karshen rikicin gabashin kasar Ukraine.

Talla

Gabannin ganawar ta yau, shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwararsa ta Jamus Angela Merkel, sun bukaci gaggauta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta din din din a yankin gabashin Ukraine mai fama da masu tada kayar baya da ke son ballewa daga kasar.

Sama da mutane dubu 10,000 suka rasa rayukansu tun bayan barkewar rikicin a yankunan Donetsk da Lugansk a watan Afrilu na 2014, biyo bayan mamaye yankin Crimea da Rasha ta yi a lokacin.

Daga bisan dai an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a garin Minsk cikin shekarar 2015, sai dai duk da haka, masu tada kayar bayan da ke son ballewa so koma Rasha, sun ci gaba da kai hare-hare kan sojin Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.