Brazil

Bolsonaro ya sha alwashin sassauta dokar mallakar bindiga

Sabon shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro. 04/12/2018.
Sabon shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro. 04/12/2018. REUTERS/Adriano Machado

Sabon shugaban kasar Brazil mai jiran gado Jair Bolsonaro da zai kama aiki a ranar 1 ga watan Janairu, ya sha alwashin sassauta dokokin mallakar bindiga a kasar, matakin da ya ce zai taimakawa mutane na gari wajen yakar manyan laifuka da kuma kariya ga dukiya da rayukansu.

Talla

A halin yanzu dokokin mallakar bindiga masu tsauri ke aiki a Brazil, wadanda a karkashinsu, tilas a yi wa wanda ke son mallakarta gwajin kwakwalwa, zalika an takaita bada lasisin mallakar bindigar ga jami’an tsaro ko ma’aikata masu alaka da su kawai.

Zalika duk wanda aka kama ya mallaki bindigar ba tare da lasisi ba, za’a daure shi tsawon shekaru 4.

Bincike ya nuna cewa, bayan kafa dokokin masu tsauri domin takaita mallakar bindigar, an samu raguwar kisan gilla a kasar ta Brazil da kashi 8, yayin da ‘yan sanda suka kwace bindigogi kimanin dubu 500,000 daga hannun jama’a.

Kididdigar da bankin duniya ya fitar, ta bayyana Brazil a matsayin kasa ta 8 a duniya da aka fi yi wa mutane kisan gilla, yayin da a bangare guda, hukumomin tsaron kasar suka wallafa rahoton da ya ce a shekarar 2017 an aikata laifukan kisan gilla dubu 63 da 883 a sassan kasar, kwatankwacin hallaka mutane 175 a kowace rana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.