Faransa

Faransa na cikin shirin ko ta kwana kan Brexit - Philippe

Fira Ministan kasar Faransa, Edouard Philippe.
Fira Ministan kasar Faransa, Edouard Philippe. Christophe Ena/Pool via REUTERS

Gwamnatin Faransa, ta kaddamar da shirin kare kanta daga koma bayan da za ta fuskanta ta fuskoki da dama, musamman tattalin arziki, muddin Birtaniya ta fice daga cikin kungiyar kasashen Turai EU, ba tare da cimma yarjejeniya ba.

Talla

Fira MInistan Faransa Edouard Philippe ya bayyana daukar matakin Yau Alhamis, bayan kammala taron ministocin kasar da ya jagoranta, wanda cikinsa suka tattauna kan matakin da majalisar dokokin Birtaniya ta dauka na yin watsi da Yarjejeniyar Brexit da Birtaniya ta cimma da Kungiyar kasashen Turai EU.

Shirin kariyar da Faransa ta dauka dai, ya tanadi kudi dala miliyan 56, wanda za ta yi amfani da shi, wajen inganta ilahirin tashoshin jiragen ruwa, da filayen jiragen saman kasar, ta fuskokin bincike da wasu kayan aikin.

Shirin zai mayar da hankali kan tashoshin jiragen saman da na ruwa ne, la’akari da cewa sune bangarorin da fitar Birtaniya daga kungiyar kasashen turai ba tare da cimma yarjejeniya ba zai fi shafa, ta fuskokin shige da ficen ‘yan kasashen 2, cinikayya, sha’anin tsaro, da sauran batutuwa masu muhimmanci.

A karkashin shirin, Faransa za ta kuma dauki karin, jami’an Kastam da likitocin duba lafiyar dabbobi 580.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI