Italya

Sojojin ruwan Italiya sun ceto bakin haure

Wasu daga cikin yan cin rani a Italiya
Wasu daga cikin yan cin rani a Italiya REUTERS/Darrin Zammit Lupi

Sojojin ruwan kasar Italiya sun ce wasu baki 3 sun mutu, yayin da wasu 15 suka bata lokacin da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a teku.Admiral Fabio Agostini yace jami’an sa sun kai dauki da jirgin sama inda suka ceto mutane 3 da aka kais u zuwa Lampedusa bayan sun hango jirgin mai dauke da mutane 20 na neman taimako.

Talla

A cikin makon da ya gabata ne Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou da Firaministan Italiya Giuseppe Conte suka sanar da samun gagarumin ci gaba a yakin hadin gwiwar da su ke da kwararar bakin haure ba bisa ka’ida ba zuwa nahiyar Turai ta Jamhuriyyar Nijar.

Shugabannin biyu sun kuma sha alwashin ci gaba da yakin don dakile bakaken fatar da ke tsallaka Turai da nufin samun rayuwa mai inganci, inda Conte ya bukaci kasashen na Turai su kara yawan ayyukan tallafawa rayuwar Afrikawa don hana su kaura.

Admiral Agostini yace sun kuma gano gawawaki 3 na yawo a sama ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI