Amurka-Mexico

Trump yayi tayin baiwa bakin-haure miliyan 1 kariya

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. AFP

Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi tayin bada kariya ta wucin gadi, ga bakin-hauren da ke cikin kasar miliyan daya, daga maida su zuwa kasashensu, amma fa idan 'yan majalisa, ta amince da bashi kudin ginin katafariyar katanga tsakanin Amurka da Mexico.

Talla

Shugaba Trump na neman amincewar majalisar dokokin Amurka kan amfani da dala biliyan 5 da miliyan 7 don gina katangar tsakaninsu da Mexico.

Bakin-hauren da kariyar ta shugaba Trump za ta shafa, sun hada da kananan yara dubu 700,000 da suka samu zama a kasar bayan shiga a matsayin baki, sai kuma wasu bakin dubu 300, da wa’adin izinin zamansu cikin Amurkan ya kare.

Tayin da Trump ya gabatar a jiya Asabar, yunkuri ne na kawo karshen rufewar wasu ma’aikatun kasar na wucin gadi, da a yanzu aka shiga rana ta 29, lamarin ya bar ma’aikata akalla dubu 800 ba tare da albashi ba.

Gurguncewar da ma’aikatun kasar ta Amurka su ka yi na wucin gadi, ya zama mafi tsawo da aka taba gani a tarihin kasar.

Rabon da ga irin wannan mataki na dakatar da ayyukan muhimmai daga ma’aikatun na Amurka, a dalilin sabanin Majalisar da bangaren zartaswa, tun a shekarar 1995 zuwa 1996, a zamanin mulkin Bill Clinton, lokacin da ma’aikatun suka shafe kwanaki 21 suna cikin yanayi na dakatar da ayyukansu na wucin gadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.