Birtaniya-Faransa

Faransa na zawarcin kamfanonin da ke shirin barin Birtaniya

Faransar dai na harin wasu kamfanoni akalla 50 da suka kunshi na kera motoci da kuma masana’antun sarrafa magunguna wadanda yanzu haka su ke shirye-shiryen barin Birtaniya bayan kammala ficewarta daga kungiyar tarayyar Turai EU.
Faransar dai na harin wasu kamfanoni akalla 50 da suka kunshi na kera motoci da kuma masana’antun sarrafa magunguna wadanda yanzu haka su ke shirye-shiryen barin Birtaniya bayan kammala ficewarta daga kungiyar tarayyar Turai EU. Michel Euler/Pool via REUTERS

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na jagorantar zagaye na biyu na taron kasuwanci yau a birnin Paris da ke da nufin janyo hankalin masu zuba jari na kasashen duniya, a wani mataki na bunkasa tattalin arzikin kasar.Sai dai taron na zuwa dai dai lokacin da shugaba Macron ke ci gaba da fuskantar tarnaki a gwamnatinsa musamman daga masu zanga-zanga da suka shafe mako 10 suna gangami a sassan kasar.

Talla

Taron dai shi ne zagaye na biyu bayan na watan Janairun bara wanda ke da nufin janyo hankalin kamfanoni, bankuna da kuma masana’antun da yanzu ke Birtaniya dawowa Faransa da harkokinsu bayan ficewar Birtaniyar daga EU.

Faransar dai na harin wasu kamfanoni akalla 50 da suka kunshi na kera motoci da kuma masana’antun sarrafa magunguna wadanda yanzu haka su ke shirye-shiryen sauya matsugunai daga Birtaniya zuwa wata kasa daban a nahiyar Turai.

Yanzu haka dai akwai akalla shugabannin manyan kamfanonin duniya 150 da suka halarci taron wanda Shugaba Macron ke karbar bakonci a fadar Versailles ciki har da shugabannin kamfanonin Uber da Snapchat wadanda ke kan hanyarsu ta halartar taron tattalin arziki a birnin Davos na Switzerland.

Sai dai duk hakan Macron na ci gaba da fuskantar suka daga bangarorin adawa baya ga dubunnan masu zanga-zanga da ke kawo tarnaki ga tattalin arzikin kasar.

Yanzu haka dai tattalin arzikin Faransar da ya kai maki 2 da digo 2 a 2017 ka iya raguwa zuwa maki 1 da digo 5 cikin shekarar nan sakamakon illar da zanga-zangar ta haifarwa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.