Birtaniya-Netherlands

Kamfanoni 250 daga Birtaniya za su sauya matsuguni zuwa Netherlands

Hukumomin kasar Netherlands sun ce yanzu haka suna tintibar manyan kamfanoni daban daban 250 da ke da cibiya a Birtaniya domin ganin sun mayar da ofisoshin su zuwa kasar sakamakon shirin ficewar ta daga kungiyar kasashen Turai.

Firaministan Netherlands Mark Rutte.
Firaministan Netherlands Mark Rutte. REUTERS/Michael Kooren
Talla

Gwamnatin Netherlands da ta sanar da wannan labari, ta ce a watan Fabarairu mai kamawa za ta bayyana tabbataccen adadin kamfanonin da za su sauya shekar, inda ta ke cewa kamfanonin sun hada da manya da kuma kanana.

Mai Magana da yawun hukumar kula da zuba jari, Michiel Bakhuizen ya ce cikin kamfanonin sun hada da kamfanin lantarkin Sony na Japan tare da Panasonic.

Yayin da Firaminista Mark Rutte ke cewa basa kallon ficewar Birtaniya daga Turai a matsayin damar inganta kasuwanci, lokacin da ya karbi Firaministan Japan Shinzo Abe, gwamnatin Netherlands na janyo hankalin kamfanonin da ke Birtaniya wajen ganin sun koma kasar.

Bakhuzien ya ce kamfanonin da su ka tintiba a shekarar 2017 sun kai 80, yayin da adadin su ya tashi zuwa 250 ya zuwa yanzu.

Masana tattalin arziki sun bayyana cewar, ficewar Birtaniya daga Turai zai haifar mata da asara sosai a bangaren tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI