Venezuela

Jagoran 'yan adawa yayi watsi da tayin tattaunawa da Maduro

Jagoran ‘yan adawar Venezuela Juan Guaido, da ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa.
Jagoran ‘yan adawar Venezuela Juan Guaido, da ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasa. France24

Jagoran ‘yan adawar Venezuela Juan Guaido da ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasar, na ci gaba da matsawa shugaba Nicolas Maduro ya yi murabus.

Talla

Wannan na zuwa a dai dai lokacin da wasu kasashen duniya ke kira ga shugaba Maduro ya soke zaben watan Mayu na bara da ya bashi wa’adi na 2, ya kuma shirya sabon zabe nan da ‘yan kwanaki, wanda zai karbu ga kowa.

A karshen makon nan dai sai da Nicolas Maduro yayi yunkurin tattaunawa da jagoran ‘yan adawa Juan Guaido, amma hakan bai yiwu ba, dalilin watsi da tayin da madugun ‘yan adawar yayi, tare da kiran dubban ‘yan kasar su ci gaba da zanga-zanga har sai an kawar da gwamnatin Maduro.

Zuwa yanzu mutane 26 suka hallaka a Venezuela sakamakon arangama da ‘yan sanda, tun bayan soma sabuwar zanga-zangar neman kawar da shugabancin Nicolas Maduro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI