Amurka

An kawo karshen rufewar ma'aikatun Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. AFP

Shugaban Amurka Donald Trump, ya kawo karshen rufewar da ma’aikatun kasar suka yi, mafi tsawo da aka taba gani a tarihi.

Talla

An kawo karshen gurguncewar ma’aikatun bayan cimma wata yarjejeniya tsakanin Trump da ‘yan majalisar dokokin na Amurka.

Sai dai ma’aikatun za su ci gaba da aiki ne tsawon makwanni 3 kawai, muddin aka gaza warware takaddama tsakanin shugaban na Amurka da ‘yan majalisu, kan bukatarsa ta neman dala bliyan 5 don gina katanga mai fadin kilomita sama da dubu 3 tsakaninsu da Mexico, bukatar da suka ki amincewa da ita.

Rufewar ma’aikatun na wucin gadi, ya gurgunta muhimman ayyuka a Washington, dakatar da sufurin jiragen sama, da kuma shafar ma’aikatan gwamnati a matakin tarayya sama da dubu 800, wadanda suka shafe makwanni 5 babu albashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.