Rasha-Turai

Rasha ta soki goyan bayan kasashen Turai ga Guaido na Venezuela

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin Alexander Nemenov/Pool via REUTERS

Kasar Rasha ta yi mummunar suka kan matakin kasashen Turai da suka amince da Juan Guaido a matsayin shugaban riko, inda take zargin su da katsalandan a harkokin cikin gidan wata kasa.

Talla

Mai Magana da yawun shugaba Vladimir Putin, Dmitry Peskov ya ce yunkurin halarta shugabancin Guaido da kuma kawar da Nicolas Maduro daga karagar mulki katsalandan ne kai tsaye wanda ba zai haifar da zaman lafiya ba.

Peskov ya ce yan kasar Venezuela ne kawai za su iya warware matsalar kasar su ta hanyar da su ke so.

A bangare guda itama Majalisar Dinkin Duniya ta ce baza ta goyi bayan kowanne bangare a kasar ta Venezuela ba.

Tuni dai kasashen Turai da Amurka suka nuna goyon bayansu ga Juan Guaido jagoran adawa wanda ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.