Isa ga babban shafi
Faransa

Apple ya biya harajin Euro miliyan 500 a Faransa

Apple ya biya bashin harajin Euro miliyan 500 a Faransa
Apple ya biya bashin harajin Euro miliyan 500 a Faransa REUTERS/Yuya Shino
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 2

Kamfanin Apple na Amurka ya cimma yarjejeniya da gwamnatin Faransa domin biyan bashin harajin shekaru goma da suka wuce. Wannan na zuwa ne bayan Faransa ta jagoranci shirin kasashen Turai na lafta haraji mai yawa kan manyan kamfanonin fasaha.

Talla

Jaridar Faransa ta L’Express da ake wallafa wa da duk mako, ta rawaito cewa, Kamfanin Apple ya biya kusan Euro miliyan 500 cikin sirri domin warware takaddamar bashin harajin.

Koda yake Apple ya ki bayyana takamammen abin da ya biya, amma wata kwakkwarar majiya ta tabbatarwa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, kudin ya kai Euro miliyan 500.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar, Apple din ya ce, yana sane da muhimmancin rawar da haraji ke takawa a tsakanin al’umma kuma yana biyan kudin harajinsa a dukkanin kasashen da yake da cibiyoyi .

Gwamnatin Faransa dai ta ki yin cikakken bayani game da wannan batu, in da take cewa, ba za ta wuce makadi da rawa ba domin kuwa akwai dokokin sirri a game da al’amuran da suka shafi biyan haraji.

Apple dai na daya daga cikin manyan kamfanonin fasaha na Amurka da ke shan caccaka a kasashen Turai saboda yanayin biyan harajinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.