Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta karfafa tsaron hanyoyin sadarwa

Kasashen Turai sun ki bai wa kamfanin Huawei damar shiga a dama shi wajen inganta hanyar sadarwar 5G
Kasashen Turai sun ki bai wa kamfanin Huawei damar shiga a dama shi wajen inganta hanyar sadarwar 5G Robyn Beck / AFP
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Bashir Ibrahim Idris
Minti 2

Gwamnatin Faransa ta ce, nan kusa za ta gabatar da wani shirin karfafa tsaron hanyoyin sadarwar wayar salula, sakamakon matakin da Amurka ta dauka na matsin lamba kan kasashen Turai domin ganin sun hana kamfanin Huawei na China gina na’urar sadarwar da ake kira 5G.

Talla

Faransa ta bayyana wannan shirin ne ta hannun Ministan Tattalin Arzikinta, Bruno Le Maire wanda ya ce, hakkin hukuma ne ta kare muradu da tattalin arzikin jama’arta, in da yake cewa 5G zai ba su damar daukar kwararan matakai a wanan fannin.

Kasashen Turai da dama sun haramtawa kamfanin Huawei na China shiga a dama da shi a shirin inganta hanyar sadarwar 5G, saboda zargin cewar, China za ta yi amfani da damar wajen kutse cikin rumbun tattara bayanan asirin kasashen.

Kasar Amurka wadda ta dauki lamarin da girma sosai, ta ce, a cikin wannan mako za ta gana da kawayenta na Turai domin ganin sun dauki matsayin bai daya kan lamarin da kuma gargadi ga China.

Wani jami’in Amurka ya ce, hulda da kamfanin sadarwar Huawei da ZTE na da matukar illa ga harkokin tsaron kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.