Isa ga babban shafi
Faransa-Ungerer

Fitaccen mawallafi kuma mai zane dan Faransa Tomi Ungerer ya mutu

Tomi Ungerer fitaccen mai zane dan gwagwarmaya kuma mawallafin littafi dan asalin kasar Faransa mazaunin Ireland
Tomi Ungerer fitaccen mai zane dan gwagwarmaya kuma mawallafin littafi dan asalin kasar Faransa mazaunin Ireland DANIEL ROLAND / AFP
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 min

Fitacen mawallafin Littafi kuma shahararren mai zane dan asalin kasar Faransa Tomi Ungerer wanda ya yi kaurin suna tsawon lokaci wajen fafutukar kare hakkin dan adam ya rasu yau Asabar a kasar Ireland ya na da shekaru 87 a duniya.

Talla

Tomi Ungerer wanda tsohon mashawarcinsa Robert Walter ya tabbatar da mutuwarsa, ya yi gwagwarmayar yaki da nuna wariyar launin fata, ka zalika ya taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kai a yakin Vietnam, haka zaben Amurka na 2015.

A cewar Robert Walter maid akin Ungerer ce ta kira shi da safiyar yau ta wayar tarho ta ke shaida masa mutuwar, wadda ta ce ya mutu tun da tsakaddaren jiya Juma’a.

A shekarar 1931 ne aka haifi Ungerer a garin Alsatian na birnin Strasbourg amma ya rasa mahaifinsa tun ya na da shekaru 3 a duniya, ya gay akin duniya na biyu lokacin da Jamus ta kwace iko da yankinsa.

A tsawon rayuwarsa da ya dauka ya na rubutun littattafai ya rubuta littafi 140 wadanda aka fassara zuwa yaruka 30 baya ga zane-zane dubu 11 wadanda yanzu haka suna ajje a wani gidan tarihi mallakinsa a Strasbourg.

Kafin komawa Ireland, Ungerer ya zauna a kasashen Amurka da Canada na tsawon lokaci kazalika ya na jin yarukan Ingilishi, Faransanci da kuma Jamusanci

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.