Jamus

Har yanzu kungiyar ISIS babbar barazana ce ga tsaro - Merkel

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel.
Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel. REUTERS/Costas Baltas

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta yi gargadin cewa, ko kusa dakarun kawancen kasashen duniya ba su yi nasarar murkushe mayakan Kungiyar ISIS ba.

Talla

Merkel wadda ta yi gargadin a wannan Jumaá a birnin Berlin, ta ce duk da rasa yankunan da mayakan na ISIS suka yi, wadanda a baya suka mamaye musamman a Syria, har yanzu Kungiyar tana tattare da babbar barazana tsaro.

Kalaman na Shugabar gwamnatin, sun ci karo da ikirarin shugaban Amurka Donald Trump, wanda a watan Disambar ya ce dakarunsa sun yi nasarar murkushe mayakan na ISIS a Syria, inda kuma yayi alkawarin janye sojojin Amurka dubu 2 da ke taimakawa mayakan Kurdawan YPG wajen yakar Kungiyar ta ISIS.

A karshen watan Afrilu da ke tafe ake sa ran kamala janyewar sojojin Amurkan dubu 2 da ke Syria, kamar yadda shugaba Trump yayi alkawari.

Sai dai matakin ya jefa kasashen yammacin Turai cikin shakku da fargabar mai yiwuwa, Kungiyar ta ISIS ta sake bayyana da cikakken karfi, bayan janyewar dakarun na Amurka, idan aka gaza cimma nasarar warware yakin basasar kasar ta Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI